Jami’in ya rasu ne yayin jagorantar farmaki a Karamar Hukumar Rimi Yan bindiga sun kashe DPO na ‘yan sanda mai kula da Karamar Hukumar Rimi a Jihar Katsina, CSP Muhammad Sani Kabir, yayin wani samame da jami’an tsaro suka kai kan masu zargin satar shanu, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana. TRT Hausa Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ta ce an hallaka ‘yan bindiga uku a yayin farmakin hadin gwiwa da jami’an tsaro da kuma al’ummar yankin suka gudanar. TRT Hausa Kwamishinan Tsaro na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa sahihan rahotanni daga shugabannin al’umma a Karamar Hukumar Rimi sun nuna shirin satar shanu a garin Magaji da ke Mazabar Maje-Gobir, lamarin da ya sa DPO din ya gaggauta tattara jami’an tsaro zuwa yankin. TRT Hausa Sanarwar ta ce ‘yan bindigar sun kai farmaki Magajen Gobir, inda aka yi artabu har zuwa asubahi, kuma aka samu nasarar kwato mafi yawan shanun da aka sace. TRT Hausa A wasu artabun da suka biyo baya a yankunan makwabta, an harbe wasu maza biyu da wasu ‘yan mata da dama, duk da cewa an sake kwato yawancin dabbobin da aka sace sakamakon hadin gwiwar al’umma da jami’an tsaro. TRT Hausa Mu’azu ya ce a wani artabu na gaba, bindigar DPO din ta samu matsala, inda jagoran ‘yan bindigar mai suna Maigemu ya harbe shi har lahira. TRT Hausa Ya kara da cewa jami’an tsaro uku da suka jikkata na jinya a Asibitin Koyarwa na Katsina, yayin da aka kai gawar jami’in da ya rasu zuwa Kaduna domin yi masa jana’iza. TRT Hausa
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
'Yanbindiga sun kashe DPO na 'yansandan Nijeriya a Jihar Katsina
Jami’in ya rasu ne yayin jagorantar farmaki a Karamar Hukumar Rimi Yan bindiga sun kashe DPO na ‘yan sanda mai kula da Karamar Hukumar Rimi a Jihar Katsina, CSP Muhammad Sani Kabir, yayin wani samame da jami’an tsaro suka kai kan masu zargin satar shanu, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana. TR...

Jami’in ya rasu ne yayin jagorantar farmaki a Karamar Hukumar Rimi Yan bindiga sun kashe DPO na ‘yan sanda mai kula da Karamar Hukumar Rimi a Jihar Katsina, CSP Muhammad Sani Kabir, yayin wani samame da jami’an tsaro suka kai kan masu zargin satar shanu, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana. TR...
