Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

'Yan tawayen M23 sun sanar da tsagaita wuta a Jamhuriyar Kongo

'Yan tawayen M23 waɗanda suka ƙwace wani babban birni a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyar Kongo sun sanar da tsagaita wuta, inda suka ce sun yi haka ne saboda jin ƙai, amma babu wasu alamu da ke nuna za su haƙura da birnin Goma, birnin da ke da ma'adinai na tiriliyoyin daloli. Sanarwar na zuwa ne...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:07
'Yan tawayen M23 sun sanar da tsagaita wuta a Jamhuriyar Kongo
Bu haberde ne var?

'Yan tawayen M23 waɗanda suka ƙwace wani babban birni a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyar Kongo sun sanar da tsagaita wuta, inda suka ce sun yi haka ne saboda jin ƙai, amma babu wasu alamu da ke nuna za su haƙura da birnin Goma, birnin da ke da ma'adinai na tiriliyoyin daloli. Sanarwar na zuwa ne...

'Yan tawayen M23 waɗanda suka ƙwace wani babban birni a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyar Kongo sun sanar da tsagaita wuta, inda suka ce sun yi haka ne saboda jin ƙai, amma babu wasu alamu da ke nuna za su haƙura da birnin Goma, birnin da ke da ma'adinai na tiriliyoyin daloli. Sanarwar na zuwa ne a ranar Litinin, jim kaɗan bayan Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa aƙalla mutum 900 sun rasu a makon da ya gabata sakamakon yaƙin da ake yi tsakanin 'yan tawayen M23 da kuma dakarun ƙasar Kongo bayan 'yan tawayen sun ƙwace iko da birnin Goma, birni mai mutum miliyan biyu. Daga baya an bayar da rahoton cewa 'yan tawayen sun ci gaba da tafiya zuwa babban birnin wani lardi, wato birnin Bukavu, inda suka lashi takobin ci gaba da yin gaba har zuwa Kinshasa, babban birnin Kongo. "Ya kamata a sani cewa ba mu da wata manufa ta ƙwace iko da Bukavu da sauran yankuna. Sai dai muna ƙara jaddada sadaukarwamu wurin karewa da kiyaye fararen hula," kamar yadda mai magana da yawun 'yan tawayen M23 Lawrence Kanyuka ya bayyana a wata sanarwa. Sai dai zuwa yanzu babu wani jawabi daga gwamnatin DRC game da wannan batun.