Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

'Yan takarar shugaban Iran sun tafka muhawara kan tattalin arzikin ƙasar

Ana hasashen cewa tsohon magajin birnin Tehran Mohammad Bagher Qalibaf ne zai lashe zaɓen da za a yi ranar 28 a watan Yuni sakamakon mutuwar Ebrahim Raisi a hatsarin helikwafta. 'Yan takara shida na shugabancin Iran sun mayar da hankali kan tattalin arzikin ƙasar a muhawararsu ta farko da suka kw...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:06
'Yan takarar shugaban Iran sun tafka muhawara kan tattalin arzikin ƙasar
A taƙaice

Ana hasashen cewa tsohon magajin birnin Tehran Mohammad Bagher Qalibaf ne zai lashe zaɓen da za a yi ranar 28 a watan Yuni sakamakon mutuwar Ebrahim Raisi a hatsarin helikwafta. 'Yan takara shida na shugabancin Iran sun mayar da hankali kan tattalin arzikin ƙasar a muhawararsu ta farko da suka kw...

Ana hasashen cewa tsohon magajin birnin Tehran Mohammad Bagher Qalibaf ne zai lashe zaɓen da za a yi ranar 28 a watan Yuni sakamakon mutuwar Ebrahim Raisi a hatsarin helikwafta. 'Yan takara shida na shugabancin Iran sun mayar da hankali kan tattalin arzikin ƙasar a muhawararsu ta farko da suka kwashe awanni huɗu suna tafkawa kai-tsaye ta gidan talbijin na ƙasar, gabanin zaɓen da za a yi ranar 28 ga watan Yuni sakamakon mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi da 'yan tawagarsa bakwai a hatsarin helikwafta. Muhawarar ita ce ta farko a cikin guda biyar da aka tsara gudanarwa a sauran kwanaki 10 da suka rage kafin zaɓen domin maye gurbin Raisi, na hannun-daman shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei wanda kafin rasuwarsa aka yi hasashen shi ne zai gaji shugaban mai shekara 85. 'Yan takarar sun tattauna kan tsare-tsaren tattalin arzikin Iran, wanda yake cikin mawuyacin hali sakamakon jerin takunkuman da Amurka da sauran ƙasashen Yamma suka ƙaƙaba wa ƙasar. Ebrahim Raisi: Tarihin shugaban Iran da ya rasu a hatsarin helikwafta Dukkan su sun yi alƙawarin yin bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an ɗage takunkuman tare da aiwatar da sauye-sauye ko da yake babu wanda ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai tunkari matsalar. Kazalika 'yan takarar sun yi muhawara kan hauhawar farashi da giɓin kasafin kuɗin ƙasar da kuma yaƙi da cin-hanci. Za a gudanar da zaɓen ranar 28 ga watan Yuni ne a yayin da ake ƙara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Iran da ƙasashen Yamma game da shirin Tehran na ƙera makamin nukiliya da sauransu.