Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

‘Yan sandan Nijeriya na neman Rukayya Saadina Dantata ruwa-a-jallo

Rundunar ta ce za ta ba da tukuici mai gwabi ga duk wanda ya ba da bayanai game da inda take. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce tana neman Rukayya Saadina Dantata ruwa-a-jallo. A wata sanarwar da ta fitar ta shafinta na X ranar Alhamis, rundunar ta ce ofishin mataimakin sufeto janar na ‘yan san...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:06
‘Yan sandan Nijeriya na neman Rukayya Saadina Dantata ruwa-a-jallo
A taƙaice

Rundunar ta ce za ta ba da tukuici mai gwabi ga duk wanda ya ba da bayanai game da inda take. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce tana neman Rukayya Saadina Dantata ruwa-a-jallo. A wata sanarwar da ta fitar ta shafinta na X ranar Alhamis, rundunar ta ce ofishin mataimakin sufeto janar na ‘yan san...

Rundunar ta ce za ta ba da tukuici mai gwabi ga duk wanda ya ba da bayanai game da inda take. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce tana neman Rukayya Saadina Dantata ruwa-a-jallo. A wata sanarwar da ta fitar ta shafinta na X ranar Alhamis, rundunar ta ce ofishin mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda da ke bincike kan laifuka ne yake neman Rukayya. Sanarwar ta kara da cewa ana nemanta ne kan zargin hadin baki wajen aikata laifuka da cin-amana da damfara da barazanar kisa. Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa Rukayya, mai shekara 35, ‘yar asalin jihar Kano ce duk da cewa gidan da aka santa da zama yana unuguwar Ikeja ne a jihar Legas. Ta kara da cewa za a bai wa duk wanda ya samar da bayanai kan yadda za a iya kama ta tukici mai gwabi. Seen her? Kindly reach out. pic.twitter.com/IxovWsUsGN — Nigeria Police Force (@PoliceNG) February 1, 2024