Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

'Yan sandan Kenya 400 sun tafi Haiti don aikin wanzar da zaman lafiya

"Muna alfaharin ganin tashin rukunin farko na 'Yan Sandan Ƙasarmu waɗanda za su kasance a tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya don aikin wanar da tsaro a Haiti," a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Kenya Kithure Kindiki, a wata sanarwa da ya Wata tawagar 'yan sandan Kneya guda 400 ta tashi daga bi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:06
'Yan sandan Kenya 400 sun tafi Haiti don aikin wanzar da zaman lafiya
Em resumo

"Muna alfaharin ganin tashin rukunin farko na 'Yan Sandan Ƙasarmu waɗanda za su kasance a tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya don aikin wanar da tsaro a Haiti," a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Kenya Kithure Kindiki, a wata sanarwa da ya Wata tawagar 'yan sandan Kneya guda 400 ta tashi daga bi...

"Muna alfaharin ganin tashin rukunin farko na 'Yan Sandan Ƙasarmu waɗanda za su kasance a tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya don aikin wanar da tsaro a Haiti," a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Kenya Kithure Kindiki, a wata sanarwa da ya Wata tawagar 'yan sandan Kneya guda 400 ta tashi daga birnin Nairobi ranar Talatar nan zuwa ƙasar Haiti don aikin wanzar da tsaro. 'Yan sandan, waɗanda za su jagoranci jami'an tsaro kimanin 1,000 na Majalisar Ɗinkin Duniya, za su tunkari gungun masu aikata laifuka a Haiti domin maido da zaman lafiya a ƙasar. "Muna alfaharin ganin tashin rukunin farko na 'Yan Sandan Ƙasarmu waɗanda za su kasance a tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya don aikin wanar da tsaro a Haiti," a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Kenya Kithure Kindiki, a wata sanarwa da ya fitar. Ya ƙara da cewa manyan jami'an 'yan sanda na ƙasar Kenya da kuma jami'ai daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ne suka halarci bikin tashin 'yan sandan zuwa ƙasar da ke yankin Caribbea. Tawagar ta ƙunshi zaratan 'yan sanda na rundunoni na musamman na Kenya waɗanda suka haɗa da Sashen Kai Ɗaukin Gaggawa da Sashen Gudanarwa da kuma 'yan sandan gama-gari. A yayin da yake jawabi gabanin tura 'yan sandan a Kwalejin Horas da 'yan sanda da ke Embakasi, Shugaban Kenya William Ruto ya ce, "Kenya tana da tarihin jajircewa a aikin wanzar da zaman lafiya da magance rikici a duniya. Zuwan 'yan sandanmu Haiti zai kawo sauƙi ga rayuwar maza da mata da yara da suka tagayyara sakamakon rikicin 'yan bindiga." Ya ƙara da cewa, "Za mu yi aiki da ƙasashen duniya domin maido da zaman lafiya mai ɗorewa a Haiti." Haiti ta kwashe shekaru da dama tana fama da rikicin 'yan bindiga. Lamarin ya yi ƙamari a watanni baya bayan nan, inda 'yan bindiga suka riƙa sace mutane da kashe su da aikata migayun ayyuka.