Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

'Yan sanda za su yi bincike kan harin da aka kai wa ayarin motocin Abubakar Malami a Kebbi

A ranar Litinin ne wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai wa ayarin motocin Malami hari, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa mutane da dama sun koma jam’iyyar haɗaka ta ADC da tsohon Ministan Shari’ar ke daga cikin manyan jagororinta. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Muhammad Sani Bello y...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:06
'Yan sanda za su yi bincike kan harin da aka kai wa ayarin motocin Abubakar Malami a Kebbi
Bu haberde ne var?

A ranar Litinin ne wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai wa ayarin motocin Malami hari, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa mutane da dama sun koma jam’iyyar haɗaka ta ADC da tsohon Ministan Shari’ar ke daga cikin manyan jagororinta. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Muhammad Sani Bello y...

A ranar Litinin ne wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai wa ayarin motocin Malami hari, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa mutane da dama sun koma jam’iyyar haɗaka ta ADC da tsohon Ministan Shari’ar ke daga cikin manyan jagororinta. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Muhammad Sani Bello ya ce ba wanda a ka kama zuwa yanzu dangane da harin da aka kai wa ayarin motocin tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami. CP Bello ya shaida wa manema labarai bayan wani taron tsaro da gwamnan jihar ya yi, cewa lamarin da ya faru a kewayen unguwar GRA, ya na da alaƙa da wasu ‘yan daba ne masu ala ƙ a da wata ƙungiyar siyasa. Kwamishinan ya ƙara da cewa, wasu ‘yan siyasa ma suna karya dokar hana amfani da jiniya da kuma yin ya ƙ in neman za ɓ e ba tare da izini ba. Ya bayyana cewa an samar da matakan tsaro domin tabbatar da bin doka da oda, yayin da ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su kwantar da hankalinsu. Ya jaddada cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kuma duk wanda aka samu da laifi za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya.