Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 13 tare da ƙwato muggan makamai a Nijeriya

Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ta ƙasa ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Litinin ta ce hakan na cikin nasarorin da rundunar ta samu a baya bayan nan a ƙoƙarinta na inganta tsaro da daƙile munanan ayyuka a faɗin ƙasar Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:06
‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 13 tare da ƙwato muggan makamai a Nijeriya
Кратко

Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ta ƙasa ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Litinin ta ce hakan na cikin nasarorin da rundunar ta samu a baya bayan nan a ƙoƙarinta na inganta tsaro da daƙile munanan ayyuka a faɗin ƙasar Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa...

Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ta ƙasa ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Litinin ta ce hakan na cikin nasarorin da rundunar ta samu a baya bayan nan a ƙoƙarinta na inganta tsaro da daƙile munanan ayyuka a faɗin ƙasar Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa ta yi nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane su 13, a yayin da jami’an Tawagar Leƙen Asiri ta Gaggawa wato IRT suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Edo don gudanar da wani aiki na musamman. Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ta ƙasa ACP O lumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Litinin, ta ce hakan na cikin nasarorin da rundunar ta samu a baya bayan nan a ƙoƙarinta na inganta tsaro da daƙile munanan ayyuka a faɗin ƙasar. “A ranar 11 ga Maris din 2025, da misalin karfe 6:30 na yamma, jami’an hukumar leƙen asiri ta IRT suna wani aiki na musamman a kan hanyarsu ta zuwa jihar Edo, sai suka ci karo da wani kwanton ɓauna da masu garkuwa da mutane suka yi a Oshara Ganden, da ke kan iyakar jihohin Kogi da Edo,” in ji sanarwar. Ta ƙara da cewa “Da suka nuna ƙwarewa ta musamman, jami'an sun yi galaba a kan maharan, wanda ya yi sanadin kama mutane takwas da muggan makamai da suka haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya da jigidar harsasai 29 da wata bindiga ƙirar Isra’ila da sauran wasu muggan makaman da kuma babur guda biyu.” Rundunar ‘yan sandan ta ce waɗanda ta kama ɗin su ne Tukur Salisu da Sani Abubakar da Mamud Sani da Umar Abdullahi da Salisu Mohammed da Salisu Usman da Bashir Audu da kuma Jibril Haruna . Kame na biyu A wani samame na daban a ranar 27 ga watan Junairu n 2025, rundunar ta ce jami’an IRT sun yi aiki da sahihan bayanan sirri inda suka kama wani Yakubu Musa da Usman Musa, dukkansu daga jihar Kaduna. Ana zargin suna da alaka da jerin garkuwa da mutane da satar shanu da ake yi a yankunan Soba da Ikara na jihar. “ A lokacin da aka kama su, an ƙwato bindigogin AK-47 guda uku da harsas ai 19, wanda hakan ke ƙ ara tabbatar da cewa suna da hannu wajen aikata miyagun laifuka,” a cewar rundunar ‘yan sandan. Kame na uku Sai kuma a ranar 21 ga watan Janairun 2025, an kama wasu mutum uku Abubakar Lawan da Isiaku Abdullahi, da Abbas Maisaude da laifin hada baki da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma garkuwa da mutane. Wadanda ake zargin sun amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama a fadin Rijana da Lambata da Dandume, da Ugama a jihohin Kaduna da Neja. Abubuwan da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da bindiga ƙirar AK-49 daya da AK-47 guda biyu, da jigidar harsasai guda 28. ‘Yan sandan sun ce ana ci gaba da kokarin kama wasu karin mambobin na kungiyarsu, in ji ‘yan sanda. Rundunar ‘yan sandan ta ce nasarar da aka samu a w adannan ayyuka ta nuna irin jajircewar da rundunar ‘yan sandan N i jeriya ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyi. Ta kuma yi kira ga ‘yan kasar da su bai wa ‘yan sanda goyon baya ta hanyar ba da sahihan bayanai kan lokaci, domin hadin kansu na da matukar muhimmanci wajen yaƙi da miyagun laifuka. “ Ga wadanda suka zabi rayuwar aikata laifuka kuwa , r undunar ta jajirce a kan aikinta na samun adalci. M asu aikata laifuka ba za su samu mafaka ba a Nijeriya,” in ji rundunar.