Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

'Yan sanda sun kama gawurtattun masu garkuwa da mutane a Abuja

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewar baya ga masu garkuwa da mutane, dakarunsu sun kama mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a babban birnin na Nijeriya. Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kama wasu masu aikata laifuka a Abuja, ciki har da gawurta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:06
'Yan sanda sun kama gawurtattun masu garkuwa da mutane a Abuja
De un vistazo

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewar baya ga masu garkuwa da mutane, dakarunsu sun kama mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a babban birnin na Nijeriya. Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kama wasu masu aikata laifuka a Abuja, ciki har da gawurta...

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewar baya ga masu garkuwa da mutane, dakarunsu sun kama mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a babban birnin na Nijeriya. Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kama wasu masu aikata laifuka a Abuja, ciki har da gawurtattun masu garkuwa da mutane. Rundunar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Asabar da maraice. Kakakin rundunar ta 'yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya gabatar wa manema labarai mutum 16 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ya ce sun kama makamai da dama ciki har da mashingan. "A cikin wadanda ake zargi da garkuwa da mutane da aka gabatar da su a yau akwai mutum uku da ke zaune a yankin Bwari - Idris Ishaku da Bala Umar da Dahiru Salisu, kowanensu dan shekara 27. Su ne suka yi jerin fashi da makami da satar jama'a a Karamar Hukumar Bwari da sauran sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja," in ji Adejobi. PRESS RELEASE LAUNCH OF SIS CONSOLIDATES FCT SECURITY ARCHITECTURE As NPF Arrests Bwari-Based Kidnappers, Parades 16 Suspects for Kidnapping, Violent Crimes, Recover GMPG, Other Sophisticated Firearms Following the recent launch of the Special Intervention Squad (SIS) by the… pic.twitter.com/Kfjw5Q8THc — Nigeria Police Force (@PoliceNG) January 20, 2024 Ya kara da cewar dakarun nasu sun kuma kama mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a babban birnin na Nijeriya. Labarai masu alaka: Chinaza Phillip: An kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Abuja Najeebah: Yadda kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa wata matashiya ya tayar da hankali a Nijeriya Kazalika rundunar 'yan sandan ta Nijeriya ta ce dakarunta na sirri sun dakile wani yunkuri na yin garkuwa da mutane lamarin ne me ya kai ga kama gawurtattun masu satar mutanen a Bwari da makamansu. Ta ce ma'aikatanta sun kama wani mutum mai suna Everest Magaji, wanda yake sayar da makamai da yin garkuwa da mutane yayin da yake kokarin karbar kudin fansa, tana mai cewa wasu abokansa da ke da hannu a lamarin sun tsere. Sai dai ta ce an kwace makamai daga wurinsu.