Hare-haren ramuwar gayya sun yi sanadin kone-kone da gudun hijirar mazauna ƙauyuka Aƙalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu ranar Talata a hare-haren da ‘yan fashin daji suka kai wasu ƙauyuka a jihohin Katsina da Kwara, inda suka ƙona gidaje da motoci tare da tilasta wa mazauna tserewa. TRT Hausa A jihar Katsina, an kashe aƙalla mutum 20 bayan ‘yan fashin daji sun kai hari ƙauyen Doma da ke mazaɓar Tafoki a ƙaramar hukumar Faskari, inda mazauna yankin suka ce maharan sun shiga ba tare da wata tangarda ba. TRT Hausa Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Surajo Aliyu, ya bayyana harin a matsayin na ramuwar gayya kuma mafi muni cikin ‘yan watannin nan, yana mai cewa jami’an tsaro ba su samu damar isowa a kan lokaci ba. TRT Hausa Aliyu ya ƙara da cewa gawarwakin waɗanda aka kashe an kai su Tafoki domin jana’izar da aka shirya yi da safiyar Laraba, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da al’ummar Katsina baki ɗaya. TRT Hausa Ƙaramar hukumar Faskari na daga cikin yankunan da suka ƙulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan fashin daji kimanin watanni biyar da suka gabata, lamarin da ya ɗan kawo zaman lafiya kafin wannan sabon hari. TRT Hausa A jihar Kwara kuma, an kashe aƙalla mutum 10 a hare-haren da ‘yan fashi suka kai ƙauyukan Woro da Nuku a ƙaramar hukumar Kaiama da yammacin Talata. TRT Hausa Rahotanni sun ce maharan, da ake zargin sun fito ne daga gandun dajin Borgu da ke jihar Neja, sun kai harin da misalin ƙarfe 6 na yamma inda suka yi ta harbe-harbe da ƙona gidaje. TRT Hausa Gwamnatin jihar Kwara ta yi Allah wadai da harin, inda ta bayyana cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq yana bibiyar lamarin kai tsaye, tana mai bayyana harin a matsayin yunƙurin ragwaye na ‘yan ta’adda. TRT Hausa Sanarwar gwamnatin ta ce harin na da nufin raunana ƙoƙarin jami’an tsaro da kuma lalata nasarorin da aka samu kan masu garkuwa da mutane a jihar a baya-bayan nan. TRT HausA
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
‘Yan Fashi Sun Kashe Aƙalla Mutum 30 a Jihohin Katsina da Kwara
Hare-haren ramuwar gayya sun yi sanadin kone-kone da gudun hijirar mazauna ƙauyuka Aƙalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu ranar Talata a hare-haren da ‘yan fashin daji suka kai wasu ƙauyuka a jihohin Katsina da Kwara, inda suka ƙona gidaje da motoci tare da tilasta wa mazauna tserewa. TRT Hausa A...

لمحة سريعة
Hare-haren ramuwar gayya sun yi sanadin kone-kone da gudun hijirar mazauna ƙauyuka Aƙalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu ranar Talata a hare-haren da ‘yan fashin daji suka kai wasu ƙauyuka a jihohin Katsina da Kwara, inda suka ƙona gidaje da motoci tare da tilasta wa mazauna tserewa. TRT Hausa A...
