Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

'Yan bindiga sun saki mahaifiyar Rarara

Sai dai Rarara bai yi ƙarin bayani ba kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin a saki mahaifiyar tasa. 'Yan bindiga sun saki mahaifiyar fitaccen mawaƙin nan na Hausa Dauda Kahutu Rarara, makonni bayan sun yi garkuwa da ita. Rarara ne ya sanar da haka a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:06
'Yan bindiga sun saki mahaifiyar Rarara
A taƙaice

Sai dai Rarara bai yi ƙarin bayani ba kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin a saki mahaifiyar tasa. 'Yan bindiga sun saki mahaifiyar fitaccen mawaƙin nan na Hausa Dauda Kahutu Rarara, makonni bayan sun yi garkuwa da ita. Rarara ne ya sanar da haka a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram...

Sai dai Rarara bai yi ƙarin bayani ba kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin a saki mahaifiyar tasa. 'Yan bindiga sun saki mahaifiyar fitaccen mawaƙin nan na Hausa Dauda Kahutu Rarara, makonni bayan sun yi garkuwa da ita. Rarara ne ya sanar da haka a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Laraba da safe. "Cikin yarda da amincin Ubangiji, mun samu dawowar Mama cikin aminci," in ji mawaƙin. Ya miƙa "matukar godiya ga Ubangiji" sannan ya gode wa 'yan uwa da abokan "sana’ata" da masoyansa a faɗi duniya bisa addu'o'in da suka yi masa. Rahotanni sun ce 'yan bindigar da suka sace ta sun nemi a ba su naira miliyan 900 a matsayin kuɗin fansa. Sai dai Rarara bai yi ƙarin bayani ba kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin sakin mahaifiyar tasa. An sace Hajiya Halima Adamu ne a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a ƙarshen watan jiya. Lamarin ya ja hankalin 'yan ƙasar sosai musamman masu amfani da shafukan sada zumunta. Fitattun mutane ciki har da tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar na cikin waɗanda suka yi kira a saki mahaifiyar Rarara.