Wasu mutane dauke da makamai sun kashe fararen hula 21 a Jamhuriyar Nijar – An kai harin ne a ranar 5 ga watan Disamba a mahadar kan iyaka tsakanin Nijar da Mali da Burkina Faso, in ji kafar yada labarai ta gwamnati. An kashe fararen hula 21 a makon da ya gabata yayin wani hari da aka kai kan ayarin motocin jigilar kayayyaki a kusa da Tera, a yammacin Nijar, yankin da ake yawan fuskantar hare-haren mutane masu dauke da makamai, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a karshen mako. Gidan rediyon gwamnati Voix du Sahel ya tabbatar da cewa an kai harin ne a mahadar iyakar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso. "Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wa motocin da ke dawowa daga kasuwar mako-mako a Tera hari a ranar 5 ga watan Disamba, a yankin mai tazarar kilomita 12 a arewa da Tera, kusa da Bankilare," in ji shi. Sojojin Nijar na kai hare-hare da dama kan kungiyoyin jihadi a yankin Tillaberi, inda ake alakanta wadannan hare-hare da "yan ta'adda."
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
'Yan bindiga sun kashe fararen hula 24 a Jamhuriyar Nijar
Wasu mutane dauke da makamai sun kashe fararen hula 21 a Jamhuriyar Nijar – An kai harin ne a ranar 5 ga watan Disamba a mahadar kan iyaka tsakanin Nijar da Mali da Burkina Faso, in ji kafar yada labarai ta gwamnati. An kashe fararen hula 21 a makon da ya gabata yayin wani hari da aka kai kan aya...