Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Ma’aikatu Sun Koka Kan Rashin Sakar Kuɗaɗen Kasafin Kudi a Nijeriya

Ministoci da hukumomi sun ce abin ya hana aiwatar da manyan ayyukan ci gaba Ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya a Nigeria na korafin cewa ba a sakar musu kuɗaɗen da aka ware a kasafin kuɗin ƙasa ba, lamarin da ke hana aiwatar da manyan ayyukan ci gaban kasa. TRT Hausa Ministan Lafiya Farfesa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:06
Ma’aikatu Sun Koka Kan Rashin Sakar Kuɗaɗen Kasafin Kudi a Nijeriya
Bu haberde ne var?

Ministoci da hukumomi sun ce abin ya hana aiwatar da manyan ayyukan ci gaba Ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya a Nigeria na korafin cewa ba a sakar musu kuɗaɗen da aka ware a kasafin kuɗin ƙasa ba, lamarin da ke hana aiwatar da manyan ayyukan ci gaban kasa. TRT Hausa Ministan Lafiya Farfesa...

Ministoci da hukumomi sun ce abin ya hana aiwatar da manyan ayyukan ci gaba Ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya a Nigeria na korafin cewa ba a sakar musu kuɗaɗen da aka ware a kasafin kuɗin ƙasa ba, lamarin da ke hana aiwatar da manyan ayyukan ci gaban kasa. TRT Hausa Ministan Lafiya Farfesa Mohammed Ali Pate ya shaida wa majalisar dokoki cewa duk da an biya albashi gaba ɗaya, amma naira miliyan 36 kacal aka bai wa ma’aikatarsa daga cikin naira biliyan 218 da aka ware a kasafin 2025. TRT Hausa Kazalika, Mukaddashin Shugaban Nigerian Bulk Electricity Trading (NBET) Plc, Johnson Akinnawo , ya ce naira miliyan 60 ne kawai aka saki daga cikin biliyan 858 na manyan ayyuka da aka ware wa hukumar a kasafin 2025. TRT Hausa Bayan wadannan bayanai, ‘yan kasa sun fara bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta, inda fitaccen dan jarida Rufai Oseni ya ce ya kasa barci bayan jin irin ƙananan kuɗaɗen da aka saki wa Ma’aikatar Lafiya. TRT Hausa Daraktan CISLAC kuma jagoran Transparency International Nigeria , Auwal Musa Rafsanjani , ya ce kasafin kudi doka ce da zarar an sanya mata hannu, kuma rashin aiwatar da ita take dokar kasa ne. TRT Hausa Rafsanjani ya ƙara da cewa Nijeriya ta amince da ware kashi 15 cikin 100 na kasafin ƙasa ga kiwon lafiya, amma har yanzu ba a kai ga aiwatar da hakan ba, yana mai cewa hakan koma baya ne ga ci gaban ƙasa. TRT Hausa